Mark 13

Alamun Ƙarshen Zamani

1Da yake barin haikalin, ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Malam! Dubi irin manyan manyan duwatsun nan! Ka ga irin gine-ginen nan mana masu kyau!”

2Yesu ya amsa, ya ce, “Ka ga dukan manyan gine-ginen nan? Ba wani dutse a nan, da za a bari kan wani da ba za a rushe ba.”

3Da Yesu yana zaune a kan Dutsen Zaitun da yake ɗaura da haikali, sai Bitrus, Yaƙub, Yohanna da kuma Andarawus, suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, 4“Ka gaya mana, yaushe waɗannan abubuwa za su faru? Wace alama ce kuma za ta nuna cewa, duk waɗannan suna dab da cikawa?”

5Sai Yesu ya ce musu: “Ku lura fa kada wani yǎ ruɗe ku. 6Da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne shi.’ Za su kuwa ruɗi mutane da yawa. 7Saʼad da kuka ji labaran yaƙe-yaƙe da jita-jitar yaƙe-yaƙe, kada hankalinku yǎ tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru. Amma ƙarshen tukuna. 8Alʼumma za ta tasar wa alʼumma, mulki kuma yǎ tasar wa mulki. Za a yi girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam, a kuma yi yunwa. Waɗannan dai mafarin azabar naƙuda.

9“Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majamiʼu. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu. 10Dole sai an fara yin waʼazin bishara ga dukan alʼummai. 11Saʼad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shariʼa, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.

12“Ɗanʼuwa zai ba da ɗanʼuwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ʼYaʼya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su. 13Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.

14“Saʼad da kuka ga ‘abin ƙyama, mai kawo hallaka’
Dan 9.27; Dan 11.31; Dan 12.11
tsaye inda
Ko kuwa shi; haka ma a aya 29
bai kamata ba—mai karatu ya gane-to, sai waɗanda suke a Yahudiya su gudu zuwa duwatsu.
15Kada wani da yake kan rufin gidansa yǎ sauka, ko yǎ shiga gida don yǎ ɗauki wani abu. 16Kada wani da yake gona kuma yǎ koma don ɗaukar rigarsa. 17Kaiton mata masu ciki, da mata masu renon ʼyaʼya a waɗancan kwanakin! 18Ku yi adduʼa, kada wannan yǎ faru a lokacin sanyi. 19Domin waɗancan kwanakin za su zama kwanaki na baƙin ciki, waɗanda ba a taɓa yin irin ba tun farkon halitta, har yǎ zuwa yanzu, ba kuwa za a sāke yin irinsa ba. 20Da ba don Ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba wani da zai tsira. Amma saboda zaɓaɓɓu waɗanda ya zaɓa, sai ya rage kwanakin. 21A lokacin nan, in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko kuwa, ‘Duba, ga shi can!’ Kada ku gaskata. 22Domin Kiristi na ƙarya masu yawa, da annabawan ƙarya za su fiffito, su kuma aikata alamu da ayyukan banmamaki, don su ruɗi zaɓaɓɓu, in zai yiwu. 23Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.

24“Amma waɗancan kwanaki, bayan baƙin azaban nan,

“ ‘rana za ta yi duhu,
wata kuma ba zai ba da haskensa ba;
25taurari za su fāffāɗo daga sararin sama.
Za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.’
Ish 13.10; Ish 34.4


26“A saʼan nan, mutane za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin gizagizai, da iko, da ɗaukaka mai girma. 27Zai kuma aiko malaʼikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga iyakar duniya har yǎ zuwa iyakar sama.

28“To, sai ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi, ganyayensa kuma suka toho, kun san cewa damina ta yi kusa ke nan. 29Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku san cewa ya yi kusan zuwa, yana dab da bakin ƙofa. 30Gaskiya nake gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun faru. 31Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.

Ba a San Rana ko Saʼa ba

32“Game da wannan rana ko saʼa kuwa, ba wanda ya sani, ko malaʼikun da suke sama ma, ko Ɗan, sai Uban kaɗai. 33Ku yi zaman tsaro! Ku zauna a shirye! Don ba ku san lokacin da shi zai zo ba. 34Yana kama da mutumin da zai yi tafiya: Yakan bar gidansa a hannun bayinsa, kowa da nasa aikin da aka ba shi, yǎ kuma ce wa wanda yake gadin ƙofa, yǎ yi tsaro.

35“Saboda haka, sai ku yi zaman tsaro, domin ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba—ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko lokacin da zakara na cara ne, ko kuma da safe ne. 36In ya zo kwaram, kada ka bari yǎ tarar da kai kana barci. 37Abin da na faɗa muku, na faɗa wa kowa: ‘Ku yi tsaro!’ ”

Copyright information for HauSRK